ABNA24 : Dama dai kafin hakan, mataimaki shugaban rikon kwaryar soji na kasar kana kuma tsohon shugaban kwamitin ceton al’ummar kasa (CNSP) Assimi Goita, Ya shaidawa taron manema labarani cewa, za a saki shugaban rikon kwarya da firaministan, bayan da suka ajiye mukaman nasu.
Tunda farko dai an tabbatar da cewa, N’Daw da Ouane, sun mika takardunsu na yin murabus a gaban mai shiga tsakani na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) Goodluck Jonathan. Ya kuma gaskata kame jami’an biyu, kan abin da ya kira “bambanci ra’ayi dake tsakaninsu, kan tsari da abubuwan da suka shafi mika mulki.”
342/